Iran ta aike da koke ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya bayan sabon harin da Amurka ta kai kan Tsibirin Larak
Gholamhossein Darzi, jakada kuma mataimakin wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da sabon matakin da Amurka ta dauka kan Iran a cikin wata wasika da ya aike wa Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewa: “Wannan matakin na cin zarafi ya nuna keta ‘yancin kai da mutuncin yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma karya doka ta 2, Sashi na 4, ta Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.”
A cikin wasikar da ya aike wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da Shugaban Kwamitin Tsaro a ranar Litinin, Jakadan kuma Mataimakin Wakilin Dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya rubuta cewa: “Bisa ga umarnin Gwamnatin kasar yana so ya jawo hankalin Masu Martaba da membobin Kwamitin Tsaro kan sabon harin wuce gona da iri na soja da Amurka ta kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yammacin Lahadi, 30 ga watan Agusta ne na wannann shekara ta 2026, sojojin Amurka sun sake komawa ga amfani da karfi ba bisa ka’ida ba tare da bin doka ba wajen kai harin ta’addanci kan kasar Iran.