Rasha Ta Yi Wa Kasar Mozambique Tayin Taimaka Mata Ta Magance  Ta’addanci

Ministan Harkokin wajen kasar RashaSergey Lavrov wanda yake ziyarar aiki a kasar Mozambique ya yi wa gwamnatin kasar tayin taimaka mata domin ta magance barazanar

Ministan Harkokin wajen kasar RashaSergey Lavrov wanda yake ziyarar aiki a kasar Mozambique ya yi wa gwamnatin kasar tayin taimaka mata domin ta magance barazanar ta’addanci da take fuskanta.

Sojojin Kasar ta Mozambique dai suna fada da ‘yan ta’adda a yankin Arewacin kasar na Cabo  Delgado dake da arzikin man fetur.

Yankin ya fuskanci hare-hare na ta’addanci daga kungiyar mai alaka da Alka’ida akan cibiyoyi na fararen hula da na tsaro. Haka nan kuma kungiyar ta rika kashe mutane da ya hada da fille kai, kamar yada suka tilastawa dubban mutane yin hijira ta dole.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted