Iravani Ya Ce: Iran Ba Zata Mutunta Yarjejeniyar Fahimta Juna Ba Matukar Amurka Ta Yi Watsi Da Ita

Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta bi tsarin yarjejeniyar fahimtar juna ba, idan Amurka ta

Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta bi tsarin yarjejeniyar fahimtar juna ba, idan Amurka ta karya alkawuran da ta dauka

Wakilin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’id Iravani, ya jaddada cewa: Iran ba za ta dauki kanta a matsayin wacce ta daure kanta alkawuran da ta dauka a karkashin Yarjejeniyar Fahimta juna ta (MOU) ba idan Amurka ta ci gaba da karya wajibcin da ke kanta. Ya jaddada cewa duk wani yunƙuri na sake kunna tsarin “snapback” na takunkumi kan Iran ba shi da wani tushe na shari’a.

Iravani ya bayyana a lokacin zaman Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa: Amurka, Faransa, da Birtaniya suna amfani da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya don cimma manufofinsu na siyasa. Ya jaddada cewa shirin makamashin nukiliya na Iran na zaman lafiya ne kuma yana karkashin kulawar Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA).

Ya kara da cewa: Hare-haren da Amurka ta kai kan yankin Iran kwanan nan sun zama keta yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da kuma karya wani muhimmin tanadi na yarjejeniyar. Ya tabbatar da cewa: Amurka tana da cikakken alhakin duk wani sakamako na shari’a da siyasa da wadannan ayyuka za su haifar.

Ya fayyace cewa kudurin Kwamitin Tsaro Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 ya kare aiki a watan Oktoban shekara ta 2025, kuma duk wasu hanyoyi da matakan da suka samo asali daga hakan sun rasa tasirinsu na shari’a. Ya ɗauki duk wani yunƙuri na farfaɗo da tsarin “snapback” na takunkumi a matsayin haramtacciyar doka kuma keta dokokin ƙasa da ƙasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted