Baqa’i: Iran Tana Sanya Ido Kan Duk Wani Motsin Makiya A Dukkan Bangarori

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sojojin Iran suna Sanya ido kan motsin abokan gaba da lura mai tsanani Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sojojin Iran suna Sanya ido kan motsin abokan gaba da lura mai tsanani

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar a yau cewa: Sojojin Iran suna sa ido sosai kan motsin abokan gaba a gabar teku, tsibirai, iyakoki, da sauran wurare masu mahimmanci.

Baqa’i ya bayyana a yau, Asabar, a cikin wani rubutu a dandalin “X”: cewa: “Masu kare ƙasar da ke cikin rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a kan gabar tekun ƙasar, tsibirai, iyakoki, da sauran wurare masu mahimmanci, suna lura da motsin abokan gaba cikin kulawa da taka tsantsan. Su ne masu tsaron kasa da tabbatar da kwanciyar hankali na ƙaunatacciyar Iran.”

Ya ƙara da cewa: “Al’umma suna aika gaisuwa da jinjina ga dukkan mayaƙa masu sadaukarwa da masu kare ƙasa, da kuma ga rundunonin da suka sadaukar da kansu waɗanda ke da babban nauyin kare wannan ƙasa ba tare da wani sakaci ba.”

Baqa’i ya ci gaba da cewa: “Mutanen Iran suna godiya da ƙoƙarin jami’an tsaro na gaskiya, juriyarsu, da kuma sadaukarwarsu, kuma suna alfahari da kasancewarsu masu ƙarfi. Don haka dukkan mu muna roƙon Allah ya zama goyon bayan jami’an tsaro kuma mai taimaka musu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted