Rasha ta ce tana ta na sa ido sosai game da tattaunawa karo na biyu tsakanin Amurka da Iran kuma a shirye take ta taimaka wajen warware shirin nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya.
Makomar shirin nukiliyar Iran da kuma zaman lafiyar yankin na iya danganta ne kan ko Washington da Tehran za su koma kan teburin shawarwari.
Yayin da tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ta tsaya cik a baya, manyan kasashen duniya musamman Rasha da China sun yi yunkurin ganin neman farfado da tattaunawar ta diflomasiyya.
Tunda farko a makon da ya gabata Majalisar Tarayyar Rasha ta amince da yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsawon shekaru 20 a hukumance da Iran, wanda ke karfafa kawancen dogon lokaci tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka hada da tsaro, makamashi da fasaha.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar a yau Laraba cewa, zai je birnin Moscow domin kai sakon Jagoran juyin juya halin musulinci Ayatollah Ali Khamenei ga shugaba Vladimir Putin.