Shugaban Majalisar Dokokin Iran ya yi gargaɗi game da sakamakon harin da Amurka za ta kai wa kadarorin Iran
Shugaban Majalisar Dokokin Iran kuma Babban mai shiga tsakani na kasar Muhammad Baqir Qalibaf, yana magana game da sabuwar dabarar soja ta Iran, ya yi gargadin cewa: “Idan makiya sun kai hari ga kadarorin Iran, to Iran za ta kai hari ga kadarorin kamfanonin mai da iskar gas na Amurka a yankin.”
A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X, Qalibaf ya mayar da martani ga barazanar da kalamai na baya-bayan nan daga Sakataren Tsaron Amurka, Pete Higgseth, yana rubuta: “Abin sauki ne kuma a bayyane: Sarkar samar da mai da iskar gas a wannan yanki tana da fadi, mai sauƙin isa gare ta, kuma mai rauni. Kamfanonin mai da iskar gas na Amurka da ke aiki a cikin waɗannan ruwaye da wurare suma suna da rauni.”
Ya ƙara da cewa: “Idan Amurka ta kai hari ga kadarorin Iran, to lallai Iran za ta kai hari ga kadarorin Amurka. Hakika Iran ta tabbatar da haka, inda ta ruguza sansanonin sojojin Amurka waɗanda suke yankin.”