Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ya bayyana cewa: Rikicin Iran ya nuna cewa kawancen da ake da shi da Amurka bai isa ba
Dr. Majed Al-Ansari, mai ba da shawara ga Fira Minista kuma kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ya bayyana a yau Litinin cewa: Yakin da ya shafi Iran ya nuna cewa kawancen dabarun tsaro da Amurka ba ya isa ya biya bukata.
Yayin da yake jawabi a taron Hely 2026 da aka gudanar a Abu Dhabi, ya bayyana cewa: Rikicin da Iran ya nuna cewa bai kamata kasashen Larabawan yankin gabar tekun fasha su dogara kacokam kan kawancen da suka kulla da Amurka domin tabbatar da tsaron kasashensu ba.
Ya jaddada cewa: Yakin da ya auku tsakanin Amurka da Iran ya sanya matsayin kasashen yankin tekun Pasha game da yadda suke kallon barazanar da ke tattare da su cikin wani muhimmin gwaji, tare da nuna muhimmancin mayar da wannan fahimta zuwa ga hadin gwiwa da daukar matakai na bai-daya; Ya kuma yi nuni da cewa tsaron yankin tekun Pasha nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, kuma dole ne kasashen yankin su kasance muhimman abokan hulda wajen tsara duk wani shiri da ya shafi tsaronsu da makomarsu.