Wakilin iran a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a birnin biyanna yace kira da aka yi wa Tehran da ta mika wuya ga sharuddan hukumar ta IAEA ba tare da wani sharadi ba bashi da ma’ana ko kadan, adaidai irin yanayin da ake ciki.
A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X a jiya litinin wakilin na iran y ace bukatar da aka gabatarwa da Tehran bata da ma’ana,domin ta yi watsi da wannan gaskiyar cewa ita hukumar IAEA da kanta ta dakatar da aiwatar da kariya da take badawa, da kuma janye masu bincikenta daga Tehran saboda dalilai na tsaro bayan kaddamar da yaki da Amurka da isra’ila suka yi ba bisa ka’ida ba.
wakilin na iran yayi kira ga sakatare janar din hukumar IAEA Rafael Grossi cewa farko ya fara kiran masu kai hare hare wato Amurka da isra’ila da su dakatar da kai hare hare ko kuma tunani kai wa cibiyoyin nukiliya iran Hari, wannan shi ne mataki mafi muhumimmanci wajen tabbatar da kyakkyawan yanayi na aiki da mataken na IAEA
kamar yadda hukumar ta bayyana har zuwa lokacin da hukumar nukiliya ta duniya da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu iran tana da hakkin kare muradunta da kashin kanta