Yamen Za Ta Mayar Da Martani Kan Hare-haren Da Saudiya

kasar yamen tasha alwashin ci gaba da mayar da martani mai tsanani kan hare haren saudiya

kakakin rundunar sojin kasar Yamen birgediya janaral Yahya Saree ya bayyana cewa ci gaba da hare- haren da kasar saudiya ke kai wa a kasar yamen ba zai tafi haka siddan ba, kuma wannan yazo ne bayan da saudiyar ta kai hare-hare a yankuna daban daban a fadin kasar yamen

Saree ya kara da cewa kasar saudiya ta ci gaba da daukar matakin soji kan kasar yamen da kuma killacewar da tayi mata, kuma ta kashe mutane da dama a harin da takai da jiragen sama a garin al-jawf

haka zali yace dole ne kasar saudiya ta fuskanci mummuanan sakamako game da hare haren da ta kadammar kan alummar kasar Yamen , wannan bayani nasa ya zo ne bayan da jiragen yakin saudiya suka yi ruwan bamabamai a wurare daban daban a kasar yamen .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted