Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya bai wa Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya wa’adin kwanaki 7 da ya gabatar da hujja kan zargin da ya yi masa na kitsa kashe-kashe a kudancin Kaduna ko kuma ya janye kalamansa.
Ministan ya zargi tsohon gwamnan da daukar matakan da suka raba kawunan al’umma tare da rura wutar matsalar tsaro a Kaduna a lokacin da yake rike da madafun ikon jihar tsakanin 2015 zuwa 2023.
A yayin wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirin ‘Politics Today’, ministan ya bayyana wa’adin mulkin El-Rufa’i a Kaduna a matsayin guda, yana mai cewa, mazauna yankin kudancin Kaduna ba su ji daɗin kashe-kashen da aka samu ba a yankinsu karkashin mulkin tsohon gwamnan
Ministan ya kuma zargin El-Rufa’i da bada umarnin rushe gidajen mutanen da yake da takaddama da su.
A wata Sanarwa ta samu sa-hannun Hon. Mohammed Bello El-Rufa’i, babban da ga tsohon gwamnan, ta kara da cewa, iyalansa sun damu matuka da kalaman da Musa yayin a hirar da kafar talabijin ta Channels tayi da shi a ranar 3 ga watan Satumba.
Sanarwar ta yi barazanar daukar matakin shari’a muddin wa’adin kwanaki bakwai ya kare ba tare da ministan ya janye kalamansa ba.