Wani babban jami’I a kungiyar Hamas yayi suka da kakkausar murya kan hare haren da sojojin isra’ila suke ci gaba da kai wa a gabar yammacin kogin jodan ,kuma yayi tir da hukumomi masu fada aji na duniya game da gum da bakinsu da suka da suka yi kan laifukan yaki da gwamnatin mamaya ta isra’ila take yi kan falasdinawa fararen hula
Mahmud Madrawi ya bayyana cewa yin gum da baki da manyan hukumomi masu fada aji na duniya suka yi kan laifukan yaki na gwamnatin mamaya, dai dai yake da amincewa da kuma nuna goyon bayan duk ta’asar da take tafkwa, da kuma kau da kai daga hakki da yanci falasdinawa,
Haka zalika yayi kira ga alummar falasdinu da ma kungiyoyin yan gwagwarmaya da su ci gaba da jajircewa wajen tunkarar makircin da ake kullawa alummar falasdinu, da kuma ci gaba da kashe su da isra’ilake yi a gabar yammacin kogin jodan da Gaza, ya bukaci da su tsaya kyam don kare falasdinu kasarsu ta gado