Abbas Araqchi Ya Taya Sabon Sakatare Janar Din OIC Murna

ministan harkokin wajen iran yayi kira ga kungiyar OIC da ta mayar da martani da ya dace kan harin Amurka a kanta

A wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da sabon sakatare janar din kungiyar hadin kai kasashen musulmi ministan harkokin wajen kasar iran Abassa Araqchi ya jaddada game da muhimmancin kasashen musulmi su mayar da martani da ya dace kan keta hurumin kasar iran da kasar Amurka ke yi , kuma su kalubalanci yin amfani da karfi wajen kai hare-hare

Bayan ya taya hissain brahim taha murnar nada shi a matsayin mukamin sakatare janar na kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC  da ka yi , yayi masa fatan samu nasara a sabon mukamin da aka bashi, kuma Araqchi ya nuna fatansa na ganin sabon sakatare janar din yayi bakin kokarinsa wajen kara samar da hadin kai tsakanin kasashen musulmi don tunkarar kalubale dake fuskantar duniyar musulunci baka diya

A lokacin tattaunawar ta su ministan wajen Iran ya yi wa sabon sakatare janar din karin bayani game da ci gaba da aka samu a baya bayan nan kan hare haren Amurka da HKI kan iran, kuma yayi ishara game da bukatar da ake da ita na mayar da martanni da ya dace daga kasashen musulmi kan keta hurumin kasar iran da aka yi, da kuma muhimmancin kalubalantar yin amfani da karfi wajen kai mata hare-hare

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted