Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran ya yi gargaɗi ga kasar Koriya ta Kudu
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar da cewa: Babu wata ƙasa mai zaman kanta, kuma mai alhaki da za ta miƙa wuya ga matsin lambar Amurka na shiga cikin ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya a Tekun Farisa da Mashigar ruwan Hormuz.
A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X na harshen Koriya, yana mayar da martani ga rahotanni game da yuwuwar kasancewar sojojin Koriya ta Kudu a Tekun Farisa da Mashigar Hormuz, kakakin ya rubuta cewa: “Tarihin dangantakar da ke tsakanin Iran da Koriya ta Kudu ya wuce shekaru 64 kuma koyaushe yana kan girmama juna.”
Ya bayyana cewa: Iran tana ba da muhimmanci ga dangantakar abokantaka da Koriya ta Kudu. Duk da haka, ya ƙara da cewa, a bayyane yake cewa a cikin yanayin da ake ciki, inda mutanen Iran ke kare kansu daga zalunci da kuma mayar da martani mai ƙarfi ga laifukan yaƙi da Amurka ta aikata kan mata da yara, duk wani shiga aiki ko kasancewar sojoji na wasu ɓangarori a Tekun Farisa da Mashigan Hormuz zai zama goyon baya kai tsaye ga mai kai hari kuma zai haifar da mummunan sakamako.
Ya bayyana cewa babu wata ƙasa mai iko da alhaki da za ta miƙa wuya ga matsin lamba da kuma dabi’ar cin amana irin ta Amurka don shiga cikin ayyukan ta’addanci da manyan laifuka a kan manyan mutanen Iran.