Qalibaf: Dole Ne Amurka Ta Dage Takunkumin Da Ta Kakaba Kan Iran A Mashigar Hormuz

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Ba zai yiwu a ketare mashigar ruwan Hormuz ba alhali kuwa Iran ba za ketare ba

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Ba zai yiwu a ketare mashigar ruwan Hormuz ba alhali kuwa Iran ba za ketare ba

Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran wato Majalisar Dokokin Kasar Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Mashigar ruwan Hormuz tana ƙarƙashin ikon Iran ce, yana mai jaddada cewa: Idan Amurka ba ta ɗage takunkumin da ta kakaba wa mashigar ba, to zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar za ta tsaya gaba ɗaya.

A wata hira da aka yi da shi ta hanyar gidan talabijin, Qalibaf ya bayyana ganawar da aka yi da wani mai binciken nakiyoyin Amurka a lokacin tattaunawar Islamabad, yana mai cewa, “Sun yi aiki tukuru tare da yunƙurin Amurka na cire nakiyoyi, suna ganin hakan a matsayin saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya ƙara da cewa: “A yayin zaman Islamabad, ya shaida wa tawagar Amurka cewa: Idan mai binciken nakiyoyinsu ya motsa ko da kaɗan ne daga matsayinsa, tabbas Iran za ta yi masa luguden wuta. Don haka sun bukaci mintuna 15 domin bayar da umarnin komawa, kuma sun yi hakan.”

Shugaban majalisar ya ƙara da cewa: “Idan akwai cunkoso jiragen ruwa a mashigar a yau, to ikon sarrafa mashigar yana karkashin kulawar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.”

Ghalibaf ya ci gaba da cewa, “Amurkawa sun daɗe suna da’awar killace mashigar. Wannan shawara ce ta wauta da jahilci saboda ba zai yiwu wasu za su iya wucewa ta mashigar Hormuz ba, alhali Iran ba za ta iya ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted