Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Ba za su shigo da mai daga waje ba, yana mai jaddada cewa; kula da amfani da shi ya hana kashe dala biliyan 12
Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya bayyana cewa: Ba su buƙatar shigo da kaya daga ƙasashen waje, yana mai cewa: Idan ba a ɗauki matakan da suka dace wajen amfani a fannin samar da makamashi ba, da Iran tana kashe kudi dala biliyan 12 wajen shigo da mai daga ƙasashen waje.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Shugaban kasar Iran Mas’oud Peshkeskian, a yau (Alhamis, 18 ga watan Nuwamba) a lokacin da yake halartar taron jami’an Daliban Dakarun Sa-Kai na Basij kan muhimman batutuwa na ƙasar, ya jaddada buƙatar gyara tsarin amfani da makamashi da kuma daidaita shi da ƙa’idodin duniya, yana mai cewa: “Batun ba shine a dakatar da amfani da makamashi ba, amma babban batun shine yadda ake amfani da shi; domin a halin yanzu ana sarrafa makamashi sau uku a duniya a matsakaicinsa kuma dole ne a yi amfani da man fetur, dizal da wutar lantarki bisa ga ƙa’idodin duniya.”
Ya ƙara da cewa: “Idan za a iya sarrafa amfani da makamashi yadda ya dace, za a fito daga wannan rikicin da ƙarfi. A halin yanzu Iran ta ware mafi yawan lokacinta ga batun makamashi. Tattaunawar Dokar Tsarin Ci Gaba kuma an yi hasashen ta ne ga yanayi na yau da kullun, amma a lokacin yaƙi yana da ma’ana da matsayi daban-daban.