Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Jaridar New York Times tana amfani da kafofin watsa labarai wajen tunzura mutane zuwa ga yaki
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya rubuta a shafinsa na sada da zumunta cewa: “Ta hanyar buga wani ikirari maras tushe game da madatsun ruwa na Iran, Jaridar New York Times ta sanya kafafen yada labarai a matsayin hujjar tayar da hankali ga yaki da kuma karya ka’idojin dokokin jin kai na asali.”
Kamfanin Dillancin Labaran Mehr ya watsa rahoton cewa: Isma’il Baqa’i, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya rubuta a shafinsa na sada zumunta, don mayar da martani ga yunkurin Jaridar New York Times na wallafa ikirari marasa tushe game da alaƙar da ke tsakanin madatsun ruwa na Iran da wuraren aikin soja: “Bayan martanin da Iran ta mayar na hankali da kuma yadda jama’a suka nuna kyama ga labarin jaridar New York Times maras tushe, wanda ya nemi nuna alaƙa tsakanin madatsun ruwa na Iran da wuraren aikin soja, wannan jaridar ta gayyace shi don yin hira, wanda ya ƙi amsa gayyatarta.”
Ya ƙara da cewa: “Ta hanyar karkacewa daga ƙa’idodin aikin jarida na ƙwararru da kuma yin ikirari marasa tushe game da madatsun ruwa na Iran, Jaridar New York Times ta sanya kanta a matsayin mai tallafawa labaran masu tunzura kai hari waɗanda, a cikin yaƙin da suka yi da Iran ba bisa ƙa’ida ba, suka nuna rashin biyayya ga dokokin jin kai na duniya da ƙa’idodin ɗabi’a mafi mahimmanci.”