Araqchi Ya Tattauna Da Takwaransa Na Oman Kan Batun Yanki

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Sun tattauna a masarautar Oman kan hanyoyin hana sake barkewar yaki da kuma dakile karuwar rikici Ministan

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Sun tattauna a masarautar Oman kan hanyoyin hana sake barkewar yaki da kuma dakile karuwar rikici

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: Tattaunawar da ya yi da jami’an Oman ta tabo ci gaban yankin da kuma kokarin diflomasiyya da nufin hana sake barkewar yaki, da kuma kafa sabon tsarin tsaro na yanki mai zaman kansa wanda ba shi da tsangwama daga kasashen waje.

A wata hira da ya yi da Press TV, Araqchi ya ce ziyarar da ya kai Muscat kwanan nan ta yi nasara, ciki har da ganawa mai kyau da takwaransa na Oman da kuma muhimmin taro da Sarkin Oman. Ya kara da cewa tattaunawar ta shafi huldar kasashen biyu, ci gaban yankin, hare-haren Amurka, da kuma kokarin hana sake barkewar yaki, yana mai lura da yadda aka samu daidaito tsakanin Tehran da Muscat kan wadannan batutuwa.

Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da rawar da Oman ke takawa a yankin, yana mai nuna cewa ita ce kasa ta farko da ta shiga cikin kokarin diflomasiyya da suka dace tare da jaddada godiyar kasarsa ga wannan rawar. Ya jaddada bukatar Oman ta ci gaba da kokarinta, ganin yadda take taka rawa mai kyau a fannin diflomasiyya da warware rikici a yankin. Ya kuma bayyana cewa an gudanar da tattaunawa mai inganci game da bukatar kafa sabon tsarin tsaro mai zaman kansa a yankin, yana mai jaddada cewa dole ne a cimma tsaron yankin daga ciki, nesa da tsangwama daga waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted