Kungiyar agaji ta Oxfam ta fitar da wani rahoto dake nuna cewa kashi 99% na yankin Gaza ya gurbace ta fuskar muhalli sakamakon yaki da ke da alaka da harin sojojin Isra’ila
Rahoto ya dogara ne bisa ga hotunan tauraron dan adam, na’urar hangen nesa, da kuma nazarin kimiyya.
Harin sojojin Isra’ila ya haifar da hadarin gurbataccen iska mai yawa wanda ke barazana ga lafiyar jama’a da rayuwar mazauna Gaza.
Sannan akwai ragowar abubuwa masu fashewa, da karafa masu nauyi, da gine-gine da aka lalata, da gurbataccen ruwan kasa inji rahoton.
A cewar rahoton ayyukan sojojin Isra’ila sun samar da fiye da tan miliyan 61 na tarkace a Zirin wanda ya haifar da mummunan sakamako inji Louis-Nicolas Jandeaux, Manajan kungiyar ta Oxfam Faransa.
Kura daga gine-gine da aka lalata da sharar da ke konewa suna haifar da matsalolin numfashi da mummunan illah ga huhu ga yawan jama’ar Gaza a yau, sannan akwai babban kalubale wajen dawo da sha’anin noma da sauransu yadda ya kamata a yankin .
Oxfem ta yi gargadi inda ta ce “Dole ne a mayar da hankali kan muhimmin bangare na sake gina Gaza.”