Hukumar leken asiri na kasar Iran ta bada sanarwan wargaza tawagogin yan ta’adda har guda 4 a lardin Azarbaijan ta yamma, a yau litinin.
Tashar talabijan ta Presstv a nanTehran ta nakalto ma’aikatar na cewa, ta kama mutane 27 daga cikinsu, tare da taimakon mutane a lardin wadanda kuma suke bada hadin kai don ganin bayan wadannan ma’aikatan Amurka-da Isra’ila.
Larabarin ya kara da cewa hukumar, har’ila yau ta kama wadannan mutane tare da wasu mutane 6 wadanda aikinsu shi ne satar hanyar shogo da makamai cikin kasar don taimakawa Amurka da HKI a manufofinsu a cikin kasar.
Sanarwan ta kara da cewa sun kwace bindigogi 253, da kuma na’urar internet guda na kamfanin Starlink.
Manufar wadannan yan kungiyoyin yan ta’adda shi ne aikata ayyukan ta’addanci a cikin manya manyan biranen Iran a duk sanda suka sami umurni daga Amurka da kuma Isra’ila.
Daga karshen sanarwan tace, mutun daya daga cikin mutane 6 da aka kama suna fasakorin makamai dan kasar waje ne. Kuma suna kokarin fasa korin bindigogin Klashinkov 52, da kuma magaza 94 zuwa cikin kasar. Sun ce sun gano cewa kungiyoyin yan ta’adda masu son ballewa daga Iran ayankin Azarbaijan ta Gabas tana da bangarori 5, masu aikin leken asiri, masu ayyukan ta’addanci, masu taimaka masu, sai bangaren farfaganda da kuma musu samar masu da kudade.