Iran Ta Yi  Watsi Da Bukatar IAEA Na Binciken Wuraren A Kasar

Wani babban dan majalisar dokokin kasar Iran a kwamitin al-amuran tsaro da harkokin waje, ya bayyana cewa dagewar hukumar IAEA na sai sun gudanar da

Wani babban dan majalisar dokokin kasar Iran a kwamitin al-amuran tsaro da harkokin waje, ya bayyana cewa dagewar hukumar IAEA na sai sun gudanar da bincike a wuraren tashe makamashin uranium wadanda Amurka ta yi masu ruwan boma bomai a cikin kasar baya bisa doka don haka Iran ba zata taba amincewa jami’an hukumar su sake dawowa wadan nan wurare ba.

Hassan Qashqawi, dan majalisa kuma kakakin kwamintin tsaro da harkokin waje na majalisar, a wata hira da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Mizan na kasar Iran ya kara da cewa, bisa wace ka’ida ce Iran zata bawa hukumar IAEA damar binciken wadannan wuraren da aka yi masu ruwan boma bomai? Yace: babu wata ka’ida babu wata doka da ta fadi haka a yarjeniyar NPT ko waninsa. Don haka ko sau nawa ne suka bukaci bincike a wadannan wurare Iran ba zata taba amincewa ba, sai idan ta tabbatar da cewa an warware dukkan matsalolin da suke kewaye da hare haren da Amurka ta kai kan wadannan cibiyoyi. Wadanda suka hada da cewa akwai cikekken amince ba wanda zai sake kawowa kasar hare hare.

Amurka ta kai hare hare kan cibiyoyin tashe makamashin Uranium na kasar Iran wadanda suke Fordo, Natanza da kuma Esfahan ne, a yakin kwanaki 12 da ita da Israila suka farwa kasar Iran da shi a cikin watan Yunin shekara ta 2025.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted