A wani lokaci yau Talata ne Kotun Sasantawa ta Wassanni, za ta yanke hukunci ko wa ya yi nasara tsakanin Senegal da Morocco a gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 2025.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar takaddamar wanda ya lashe gasar tsakanin Senegal da Morocco.
Za a buga hukuncin a shafin yanar gizon na hukumar ta CAS a daidai lokacin da hukumar ta ce labaran karya sun bazu a bangarorin biyu tun lokacin da aka shigar da karar a watan Maris na 2026.
Idan ana tune, Senegal ce ta lashe wasan karshe na Kofin Afirka a Rabat babban birnin Morocco mai masaukin baki, bayan da dan wasanta Pape Gueye ya zura kwallo a karin lokaci a ranar 18 ga Janairu, saidai bayan karar hukumar kwallon kafa ta Morocco ta shigar Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta ayyana Morocco a matsayin wacce ta yi nasara, saboda janyewar da ‘yan wasan Senegal sukayi na wani dan lokaci daga filin wasan don nuna rashin amincewa da hukuncin Penalty da aka baiwa ‘yan wasan Morocco.
Bayan da CAF ta ayyana Morocco a matsayin wacce ta yi nasara Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal ta daukaka kara zuwa Kotun Sasantawa ta Wasanni (CAS).
Bayan zaman sauraren kara a ranar 8 ga Oktoba, bangarorin biyu yanzu suna jiran yanke hukunci na karshe yau Talata, wanda zai tabbatar da wanda ya zama zakaran gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka na 2025.