Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, sharuddan kasar Iran na dawo da zaman lafiya a mashigar ruwa ta Hurmuz ba masu wuya ne ga Amurka idan tana bukata, sharudda ba wadanda zasu gagareta bane, inji shi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Esma’il Bakha’ei yana fadar haka a safiyar yau Litinin ya kuma kara da cewa, Jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) tana neman hakkinta ne, don haka ba zata taba dauke sharuddanta wadanda aka cimma a birnin Islamabad ba.
Yace idan Amurka ta aiwatar da Alkawulanda ta sanyawa hannu, Iran ba zata sabawa al-kawulanda ta dauka zata yi ba. Kuma tana iya bude mashigar ruwa ta Hurmuz a cikin karamin lokaci.
Baghaei ya kara da cewa, ya san al-amarin yana da wuya ga Amurka amma kuma wannan ne maganinta, kuma lafiya ga kasar Iran. Muna son mu kawo karshen yake yake a kan JMI gaba daya.
Dangane da yiyuwar Iran ta dakatar da kai hare hare kan kayakin man fetur a kasashen yankin tekun farisa, da kuma bude mashigar ruwa ta Hurmuz kuma, ? Baghaei yace wannan zai faru ne kawai idan babu sojojin Amurka a yankin.