Tripoli Ta Nemi Ji Daga Kyiv Kan Harin Jiragen Ruwan Rasha

Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta yi kakkausar suka kan kalaman Zelensky.

Hukumomin Tripoli da na gabashin Libiya sun nemi bayani daga gwamantin Kyiv bayan kai hari kan jiragen ruwan Rasha a kusa da Benghazi.

Gwamnatin Tripoli ta nemi bayani daga Kyiv bayan hare-haren, yayin da gwamnatin gabashin kasar ta yi kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa kan zargin kasancewar sojojin Ukraine a Libya.

Gwamnatin Tripoli wacce kasashen duniya suka aminta da ita ta yi Allah wadai da hare-haren da Ukraine ta yi ikirarin kai wa jiragen ruwan Rasha kusa da Benghazi kuma ta nemi bayani daga Kyiv.

A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta yi kakkausar suka kan kalaman shugaban Ukraine Volodimir Zelensky na daukar alhakin kai hari kan jiragen ruwan Rasha a kusa da birnin Benghazi,” kuma ta yi kira ga hukumomin Ukraine “da su bayar da bayani a hukumance.”

Hukumomin gabashin Libya sun yi kira ga Majalisar ĆŠinkin Duniya, da ta gudanar da bincike kan zargin kasancewar sojojin Ukraine a Misrata, Zawiya, da kuma wasu wurare dake yammacin kasar.

Kafin nan dai Rasha ta bakin jakadan ta da ke Tripoli, ba makawa zai fuskanci maratni, yana mai cewa tabbas “Kyiv ba zata iya aiwatar da wannan aikin ba tare da goyon bayan kasashen yamma ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted