Firaministan Qatar, kana Ministan Harkokin Wajen kasar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, ya yi gargadin cewa Gabas ta Tsakiya ba za ta iya sake jure wa wani sabon tashin hankali ba a tsakanin Amurka da Iran, yayin da Doha ke kokarin farfado da tattaunawar diflomasiyya da ta tsaya cak tsakanin Tehran da Washington.
Da yake jawabi a lokacin ziyarar aiki a Washington inda ya gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio, Mista Al Thani ya jaddada cewa Doha tana jan hankalin bangarorin biyu don ci gaba da tattaunawa.
Yanayin tsaro a yankin ya tabarbare bayan yakin da Amurka da Isra’ila suka shelanta kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, A yayin da yarjejeniyar fahimtar juna da aka sanya wa hannu a Islamabad a watan Yuni ta tsaya cak.
Jerin takunkuman Amurka, toshewar tashohin jiragen ruwa na Iran, da tsaron mashigin Hormuz su ne batutuwan da bangarorin ke takaddama a kai, inda suke ci gaba da kai hare hare lokaci-lokaci.
Trump ya fada a wani taron manema labarai a Fadar White House ranar Juma’a cewa Tehran na son cimma yarjejeniya don kawo karshen rikici, yana mai dage kan cewa “muna son cimma yarjejeniya ta gaske, ba yarjejeniya ta bogi ba.”
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa Amurka da gwamnatin Isra’ila sun kasa cimma burinsu a yake-yake biyu da ba su da wani dalili kan Iran.
Sun canza daga neman Iran ta “mika wuya ba tare da wani sharadi ba” zuwa “tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba” a lokacin yaĆ™in kwanaki 12, sannan kuma zuwa “tattaunawa ba tare da wani sharadi ba” a lokacin yakin kwanaki 40 inji minsitan harkokin wajen kasar ta Iran.