Yemen: Hare Haren Jiragen Yakin Saudia A Lahij, Ta’aiz Da Hudaidah, Shahidai 10

Jiragen yakin Saudia sun kai hare hare kan lardunan Lahej Hudaida da kuma Ta’aij a kasar yemen a safiyar yau Litinin, inda hare haren suka

Jiragen yakin Saudia sun kai hare hare kan lardunan Lahej Hudaida da kuma Ta’aij a kasar yemen a safiyar yau Litinin, inda hare haren suka kai ga shahadar mutane 10 da kuma raunata wasu 20 wadanda suke jinya a asbitocin kasar.

Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto dan rahotonta a kasar yana cewa, jiragen yakin Saudia a yau litinin ta kaiwa larduna guda uku hare hare, sun kuma kashe mutane akalla 10, sannan wasu 20 sun ji rauni. Labarin yakara da cewa hare haren sun hada da guda 3 a Al-Muqatara dake lardin Lahej, sai kuma wasu 3 a Salah da ke lardin Ta’aiz.

Kamfanin dillancin labaran Saba’a na kasar Yemen ya bayyana cewa, A lardin Hudaidah, jiragen yakin Sa’udia sun kai hare hare kan wani babban gina na sadarwa a lardin .

Labarin ya kara da cewa, jiragen yakin Saudia suna kai hare hare kan kan kasar Yemen a ko wace rana a cikin yan kwanakin da suka gabata suna rusa manya manyan gine gine, manya manyan ayyuka kamar hanyoyi wuraren samar da ruwa da wuraren samar da wutan lantarki.

A maida martani sojojin kasar Yemen sukan kai hare hare cibiyoyin bada wutan Lantarki, tashoshin jiragen sama da gine ginen sojojin kasar da kuma sojojinsu a cikin kasar ta Yemen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted