Kakakin Majalisar Dokokin Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya yi watsi da rahotannin da wasu kafofin watsa labarai na Amurka suwa rawaito na zargin cewa Iran na shirin kai hari ga manyan jami’an gwamnatin Trump da bam ko makami mai guba.
Mista Ghalibaf ya yi wannan furucin ne a wani rubutu da ya yi a ranar Talata a shafinsa na X, a matsayin martani ga wani rahoto da CNN ta fitar wanda ya Ambato wani rahoto na leken asirin Amurka dake cewa Iran na tsara shirye-shiryen kai irin wannan hari a Washington, DC.
A ranar 16 ga Nuwamba, CNN ta ruwaito cewa sabbin bayanan sirri na Amurka sun nuna cewa Iran na tsara shirye-shiryen kai hari ga manyan jami’ai a cikin gwamnatin Shugaba Donald Trump ta hanyar tayar da wani abu da ake kira “bam mai datti” ko amfani da “makamai masu guba a Washington, DC.
Rahoton ya kara da cewa jami’an Amurka har yanzu suna muhawara kan ko Iran za ta iya aiwatar da irin wannan.
Washington na ci gaba da matsin lamba kan Iran ta hanyar barazanar soja, toshe hanyoyin tattalin arziki.
Tehran ta yi ta gargadi akai-akai cewa ayyukan irin wannan za su fuskanci martani mai karfi.
Jami’an Iran sun ce duk wani karin hari zai fadada yakin, yayin da suke sake jaddada shirin Jamhuriyar Musulunci na kare ikonta da tsaron yankin.