Harin Kawance Saudiyya Ya Kashe Mutane 25 A Kasar Yemen

Mutane 25 suka mutu sakamakon harin da Saudiyya ta kai wa motocin fasinja a kasar Yemen Wani harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta

Mutane 25 suka mutu sakamakon harin da Saudiyya ta kai wa motocin fasinja a kasar Yemen

Wani harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kai kan motocin bas-bas guda biyu da manyan motoci da dama a Wadi Ma’abaq, Jihar Lahaj, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 25, sannan shida suka jikkata wasu kuma suka bata.

A labarain da kamfanin dillancin labaran Mehr ya nakalto daga kafar kasar Yemen ta Al-Masirah, ya wallafa cewa: Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kai a yankin Ma’abaq da ke gundumar Al-Maqatirah a Jihar Lahaj ya karu zuwa mutane 25, inda shida suka jikkata.

Majiyoyin yankin sun sanar a ranar Talata cewa: Gawawwakin da suka kone sun ci gaba da kasancewa a cikin daya daga cikin motocin bas din da aka kai masa harin a yankin Ma’abaq, wanda hakan ya sa gano su da wahala.

WaÉ—annan majiyoyin sun kuma nuna cewa ci gaba da yawan jiragen saman yakin Saudiyya da ke kai hare-hare a wurin da aka yi kisan kiyashin Ma’abaq ya hana kungiyoyin ceto da mazauna yankin isa yankin, wanda hakan ya kara yawan wadanda suka mutu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted