Gwamnatin jihar Zamfara a arewa maso yammacin tarayyar Najeriya ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta ware Naira biliyon N1.47 don yaki da yan ta’adda wadanda suka addabi jihar. Kuma zata sami matasa wadanda zasu yi wannan aikin.
Jaridar Leadership ta Najeriya ta nakalto Dauda Lawan yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da matsan karamar hukumar tsafe a gidan gwamnati a Gusau. Ya kuma kara da cewa zai bada naira miliyon 10 ga ko wace unguwa daga unguwanni 147 da ake da su a jihar don sayan makaman da zasu kare kansu da su a duk lokacinda yan ta’adda da kuma masu garkuwa da mutane suka shigo anguwanninsu.
Sannan ko wace unguwa zata gabatar da matasa wadanda zasu sami hurswar anfani da makamai, kafin su fara aiki tsaron unguwnaninsu.
Lawal ya kara da cewa gwamnatinsa a wannan karon ba zata tattaunawa da yan ta’adda ba, zasu ci gaba da yakarsu sai sun sami nasara a kansu ko suka daina ayyukan ta’addanci. Suka mika kai.
Yace ya tattauna wannan al-amarin tare da wdanda abin ya shafa kuma sun kai ga matsaya ka cewa dole ne al-umma ta kare kanta da kanta babu tattaunawa da makasa yan ta’adda da kuma masu satar mutane.da kuma garkuwa da su.
Labarin ya kara da cewa mutanen Jihar Zamfara sun yi maraba da wannan matakin suna kuma fatan zai magance matsalolin tsaron da suka dade suna fama da su. A jihar.