Wani Sabon Rahoto Ya Bayyana cewa Najeriya ce ke kan gaba a fannin zuba jarin mai da iskar gas a Afirka, wanda jimillarsa ya kai dala biliyan 221 a fadin nahiyar.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke faɗi-tashin neman ingantaccen makamashi, lamarin da ke sake tabbatar da matsayin Najeriya a matsayin jagorar fannin makamashi a Afirka.
Rahoton wanda kamfanin binciken makamashi na Industrial Info Resources ya fitar, ya nuna cewa a halin yanzu ana bin diddigin manyan ayyukan samar da mai da iskar gas sama da 800 a kasashen Afirka daban-daban.
Najeriya na sa ran samo sabbin hannayen jarin da ya kai tsakanin dala biliyan 30 zuwa biliyan 50 nan da shekara ta 2030, ta hanyar manyan ayyukan hakar mai da iskar gas har guda 22 a cikin teku