Wani sakamako na sauraron ra’ayin jama’a da aka yi a Birtaniya ya nuna cewa mafi yawancin mutanen kasar ba su amince da a bai wa Amurka damar amfani da sansanonin sojan wannan kasar ba, domin kai wa Iran hari.
Cibiyar tattara bayanai akan ra’ayoyin mutane “Yogao” wacce ta gadudar sauraron ra’ayin al’umma, ta fitar da sakamako dake cewa; a tsakanin mutanen da aka saurari ra’ayin nasu da akwai mutane 5000 da su ka bayyana ra’ayinsu da 637 daga cikinsu, sun nuna cewa ba su amince da cewa a bai wa Amurka damar kai wa Iran hari daga sansanonin kasar ba. Wannan adadin na mutanen da su ka bayyana ra’ayin nasu,ya kai kaso 75%, daga cikinsu kaso 38% sun nuna kin amincewa.
A tsakanin wadanda su ka bayyana ra’ayin nasu da akwai wadanda sun fito ne daga fitattun jam’iyyun siyasa na kasar ta Birtaniya. Daga cikin Mabiya jam’iyyar da take Mulki a Birntani ta “Labour’ da akwai kaso 47% da su ka ce ba su yarda a bai wa Amurkan wannan damar ba. Sai kuma ‘yan jam’iyyar “Liberal Democrat” da sun kai 68%.
Gabanin wannan sauraron ra’ayin jama’ar, fira ministan kasar Birtaniya, Keir Starmer ya ki amincewa da bukatar Donald Trump ta yin amfani da wani sansaninta dake tekun India, domin kai wa Iran hari.
Mujallar “Times” ta bayar da labarin dake cewa; Birtaniya tana jin tsoron cewa bai wa Amurka damar amfani da wannan yana da sakamako ta fuskar doka.