Janar Muhsin Riza’i wanda shi ne kwamandan dakarun kare juyin musulunci a zamanin kallafaffen yaki na farko, ya ce; Idan har Amurka ta ci gaba da killace Iran, to jiragen ruwanta za su fuskanci hatsari da kuma asara mai yawa.
Janar Riza’i ya kuma ce; Wajibi ne ga Amurka da ta sauya halayyarta, idan kuwa ba haka ba, to ba za mu iya jurewa wannan yanayin ba.
Haka nan kuma y ace; Ba za mu taba bayar da dama a bude wata hanar ruwan ta daban ba a mashigar ruwan Hurmuz.
Kasashen Iran da Oman dai sun cimma matsaya akan sabuwar hanyar da jiragen ruwan za su rika wucewa ta cikinta da kuma yadda za a tafiyar da ita.