Wani Babban Jami’I A Kasar Iran Yace Jinin Jagora  Ya Farkar da alumma Iran

Wakilin jagora a majalisar koli ta tsaron kasa, Ali Akbar Ahamadiyan ya bayyana cewa jini mai tsarki na jagoran juyin musulunci ya kara farkar da

Wakilin jagora a majalisar koli ta tsaron kasa, Ali Akbar Ahamadiyan ya bayyana cewa jini mai tsarki na jagoran juyin musulunci ya kara farkar da alummar iran kuma ya tunatar da su nauyin dake wuyansu na tunkarar wulakancin kasashe ma’abota girman kai na duniya

A cikin wani jawabi da ya fitar a jiya litinin ya yi ishara game da yadda jagoran ya dinke alummar kasar da nuna musu hanyar jajircewa da rashin mika wuya ko kadan ga zaluncin duniya, domin jininsa mai tsarki ya samar da farkawa mai girma. inda suka tashi da murya daya ta nuna rashin amincewa da duk wani wulakanci

Jamai’an kasar iran suna kallon irin wannan shahadar a matsayin wani abu da ke karfafa jamhuriyar musulunci  , kuma yana jan hankalin jamaa da isar da sako dake nuna cewa jinin shahidi tamkar wani makamashi ne dake kara karfin zuciya kuma yake tabbatar da nasarar gaskiya kan girman kai da zaluncin duniya

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted