Jami’a mai kula da al-amuran harkokin wajen tarayyar turai Kaja Kallas ta zargi Iran da sabawa takardan fahintar juna tsakanin ta da Amurka wanda ya kawo karshen yaki a tsakaninsu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kallas na cewa EU a shirye take ta tabbatar da cewa an aiwatar da yarjeniyar ta Islamabad. A taron ministan basu tattauna kan cewa shin Tehran ne ko kuma Washington take sabawa takardon fahintar juna tsakanin Amurka da Iran.
Labarin ya kara da cewa dakatar da zirga zirgan jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hurmuz ta shafi tattalin arzikin kasashen turai da dama, wannan ya sa kasar Jamus ta rage ma’aikata kimani 100,000 daga kamfanin kera motoci na Volkswagen kadai.
Don haka basu fito da sunan kyautata tattalin arzikin kasashen yankin ba sai dai suka fito da cewa Iran ta sabawa MOU da Amurka, don halattawa kansu cutar da Iran ko tilasta mata bude mashigar ruwa ta Hurmuz.