A ranar jin kai ta duniya, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin karuwar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kai wa ma’aikatan jin kai a zirin Gaza, yayin da ake ci gaba da fuskantar yakin da Isra’ila take kaddamarwa kan al’ummar yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da cin zarafin ma’aikatan jin kai, wanda ya kai matsayi mafi girma a cikin 2023 tare da kashe ma’aikata 280 daga cikinsu a fadin duniya, bayanin yana gargadin cewa adadin na iya karuwa saboda tasirin yakin Isra’ila a kan Gaza.
Joyce Msuya, mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai da kuma mataimakin mai ba da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, ta ce: “haifar da tashe-tashen hankula da kuma cutar da ma’aikatan jin kai da rashin bin ka’ida ba abu ne da za a amince da su ba, kuma suna da matukar hadari ga ayyukan agaji a ko’ina a fadin duniya.
Ta ci gaba da cewa, “Yayin da aka kashe ma’aikatan jin kai 280 a cikin kasashe 33 a bara, shekrar 2023 ita ce shekarar da aka samu mafi yawan kisan ma’aikatan agaji, yayin da adadin wadanda suka mutu ya karu da kashi 137% a idan aka kwatanta da shekara 2022 inda mutane 118 daga cikin masu gudanar da ayyukan gaji suka rasa rayukansu.