Jagora: Dole Ne A Magance Matsalar Rashin Yawan Jama’a A Iran

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne a magance kurakuran da suka samo asali daga manufofin jama’a na baya A cikin wani

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne a magance kurakuran da suka samo asali daga manufofin jama’a na baya

A cikin wani sako da ya aike wa bikin bayar da lambar yabo ta matasa na kasa na hudu, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: “Ƙara yawan jama’a tare da mayar da iyali a matsayin ginshiƙi” ya zama wani tsari na dabara, kuma yana ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan ƙarfi da ci gaban ƙasar Iran; yana da matuƙar muhimmanci a magance matsalolin da suka samo asali sakamakon wasu manufofin yawan jama’a na baya.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husseini Khamene’i, Jagoran juyin juya halin Musulunci, ya tabbatar a cikin sakonsa ga bikin bayar da lambar yabo ta matasa na kasa na hudu cewa: Duk wani dan kasar Iran mai kishin kasa wanda ke fatan samun kyakkyawar makoma mai wadata ga kasarsa da mutanensa yana da kwarin gwiwa da kuma himma wajen tabbatar da ci gaba da karuwar yawan jama’ar Iran bisa ga ka’idojin wayewar Musulunci ta zamani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted