Kwararru kimani 2000 a duk fadin duniya suka rubutawa babban sakataren MDD da kuma kwamishinin hukumar mara ta majaliasar wasika inda suke bukatar a kori HKI daga hukumar.
Shafin labarai na Parstoday Farisanci ya bayyana cewa wadannan masana sun dauki wannan matakin ne bayan ko in kula da HKI take yi dangane da dakatar da kissan mata da yara a yankin kare danginda take jagoranta a yankin zirin Gaza na kasar falasdinu da ta mamaye.
Wasikar ta bukaci shuwagabannin majalisar da kuma hukumar su dauki mataki kan ta’asan da HKI take aikatawa a Gaza su kuma koreta daga kungiyar saboda kissan mata da yara da take yi a Gaza.
Kafin haka dai kotun kasa da kasa ICJ ta bukaci HKI ta dakatar da kashe mata da yara fararen hula wadanda basa dauke da makami a gaza, ta kuma kyale dukkan bukatun rayuwa su shiga yankin zirin gaza.
Har’ila yau a baya bayan nan kwamitin tsaro na MDD ya bukaci HKI ta dakatar da bude wuta a kan zirin gaza amma ta yi kunnen uwan shegu da dukkan wadannan kiraye karaye. Ya zuwa yanzu dai kashi 70 na na wadanda HKI take a gaza mata da yara ne.
Ta kuma kara da cewa cikin mutane kimani dubu 33 wadanda sojojin HKI suka kashe mata da yara ne wadanda ta jefa boma bomai kan giajensu.