Sojojin Isra’ila Na ci Gaba Da Rusa Gidajen Falasdinawa

sojojin isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a yankunan falasdinawa da rusa gidajensu

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin isra’ila sun ci gaba da keta alfarma da suka saba yau da kullum,  inda suka kai samame tare da kame falasdinawa a gabar yammacin kogin jodan  da kuma rusa gidaje da mameye yankuna a birni Qudus

Haka zalika a safiyar yau laraba ma sojojin isara’il sun kai samame kuma sun kama falasdinawa da dama kuma sun rusa gadaje da kuma mamaye wasu yankuna a yankin falasdinu, inda suka kama mutane 9 akalla, kum a sun kama wasu matasa a Ramallah da kuma wasu matasa guda 2 garin dubas,da kuma yammacin garin aqaba, kana kuma sun kama wasu mutane 5 a garin Nablus

A garin Bait lahm kuma sojojin isara’ila sun kai samame a sansanin yan gudun hijira na ayat dake gabashin yammcin falasdinu, kuma sun fada cikin gidaje masu yawa da suka hada da gidajen ismail Abdallah isa uruj da ibarahim zair da kuma shaikh Dawud hassan zair da kuma rami da safiyyi nasrullah

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted