Jawabin Shugaban Kasar Iran A Majalisar Dinkin Duniya

Shugaba kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su jin tsoron yaƙi a fagen tsaron kasarsu kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen

Shugaba kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su jin tsoron yaƙi a fagen tsaron kasarsu kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tattaunawa kan zaman lafiya

A jawabinsa a zaman babban taron Majalisar Dinkin Duniya A yau, Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshikian ya jaddada cewa: Ba za a iya tilasta wa Iran ta mika wuya ta hanyar yaƙi ba, ya ce: Iran ba ta taɓa fara wani yaƙi ba kuma koda yaushe tana nuna jajircewarta ga teburin tattaunawa. Makiya sun tilastawa Iran yaƙi, amma Iran ta tabbatar da cewa: Ba ta tsoron yaƙi don kare kanta kuma ba za ta yi watsi da tattaunawar zaman lafiya ba, kuma za ta tsaya tsayin daka don kare ƙaunatacciyar kasarsu har zuwa numfashin ƙarshe.

A lokacin jawabinsa a zaman taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81, shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba ta ganin maƙwabtanta a matsayin abokan hamayyarta na tsaro kuma tana son maƙwabtar ta kasance mai ƙarfi.

A farkon jawabinsa, Shugaban Pezeshkian yana riƙe da hotunan ɗaliban makarantan Minab da Lamerd da suka yi shahada a lokacin harin Amurka, ya ce: Jiya, Shugaban Amurka ya gaya wa duniya cewa: Iran ‘yar ta’adda ce, cewa al’ummar Iran waɗanda ta’addanci ya shafa sune ‘yan ta’addan?. Sun fito ne daga ƙasar da aka kashe shugabanninta ba tare da wani dalili ko shaida ba. Iran ce kasa ta farko da aka jefa mata bam a kan wata makaranta aka kashe kananan ‘ya’yayenta, kuma waɗannan makaman Amurkawa ne da Isra’ila. Ba su aikata wani laifi ko cuta kan wani ba. Sannan Lamerd ƙaramin gari ne a Iran inda aka jefa bam a wurin motsa jiki na yara aka kashe su.

Ya ci gaba da cewa: “Amurka ta jefa bama-bamai masu tarin yawa a can waɗanda suka kashe fararen hula sannan an aiwatar da kashe-kshen gilla wadanda suka janyo shahadan masana ilimin kimiyya na Iran, fararen hula mata da yara,  duk da cewa ba su da laifi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted