Araqchi: Iran Tana Kare Ikon Kasarta Ne Da Muradunta

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya jaddada kudurin Iran na kare ikon kasarta da muradunta Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya jaddada kudurin Iran na kare ikon kasarta da muradunta

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da Ministan Harkokin Wajen Azerbaijan Jeyhun Bayramov a ranar Talata da rana a matsayin wani ɓangare na shawarwarin da yake ci gaba da yi da ƙasashen da ke halartar taron shekara-shekara na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya.

A yayin taron, sun yi musayar ra’ayoyi kan dangantakar ƙasashen biyu tsakanin Iran da Azerbaijan da kuma ci gaban yanki da na duniya.

Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi nazari kan yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu tsakanin ƙasashensu a fannoni daban-daban na tattalin arziki da kasuwanci, da kuma batutuwan da suka shafi tsaro da haɗin gwiwa a yankin Kudancin Caucasus. Sun tabbatar da alƙawarin ƙasashensu na aiwatar da waɗannan yarjejeniyoyin da kuma ƙarfafa haɗin hadin kai da haɗin gwiwa don biyan buƙatun ƙasashen biyu.

Ministan Harkokin Wajen Iran ya kuma yi wa takwaransa bayani game da sabbin abubuwan da suka faru a Tekun Farisa da Mashigar Hormuz, yana mai jaddada ƙudurin Iran na kare ikonta da muradun ƙasa daga zalunci da matsin lamba ba bisa ƙa’ida ba daga Amurka da Haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted