Sharhi Bayan Labarai: Jawabin Dr Pezeshkiyan A MDD

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan jawabin shugaban kasar Dr Masoud Pezashkiyan a babban zauren MDD

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan jawabin shugaban kasar Dr Masoud Pezashkiyan a babban zauren MDD a ranar Laraba, wanda ni tahirmin zan karanta.

///…A ranar laraba 23 ga watan satumba na shekara ta 2026 ne shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan, ya gabatar da jawabi a gaban babban zauren MDD na shekara shekara, karo 81th.

Shugaban ya fara da sunan All..sannan kai tsaye ya haw kan shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya bude taron babban zauren a jiya, da jawabi wanda a cikinsa ya kira JMI a matsayin yan ta’adda, yake kuma barazanar zai shafeta daga doron kasa.

Wannan mutum shi ne ya kashe jagoran, Jagorammu wannan – ya daga hoton Imam Sayyid Aliyul Khaminaei’ ba tare da wani laifi ba, Amurka da HKI sun kashe wadannan yaran, sannan a Lameh sojojin Amurka da HKI sun kashe masu wasa a wannan dakin wasan, kafin haka sun kashe masanan makamashin nukliyar mu. A yake, HKI tana kashe duk wanda ta ga dama, sannan su kira mu yan ta’adda.

A ranar da aka rantsar da ni a matsayin shugaban kasa a Iran sun kashe Ismael Haniyya (shugaban kungiyar Hamas).

Don haka Iran tana kare kanta ne, kuma ta nunawa wadannan kasashen da kuma duniya kan cewa ba zata mika kai ga zalunci ba. Iran tana kare kanta da makaman da take da su, don haka kowa ya san cewa ba zai jefa bom a kan kasar Iran ba tare da  mun maida martani ba.

Shugaban ya bayyana cewa dole mu mallaki makamai don kare kammu. Iran ba zata taba amincewa a kawo makamai a bawa kasashen da suke yankimmu sannan an amfani da su a kammu ba.

Don haka Iran ba zata sake barin wadannan yan ta’adda su ci gaba da amfani da ruwa a yankimmu don hana zaman lafiya a yankin ba. Yace Iran bata tsoron shiga yaki, yaki na kare kanta har zuwa karshen numfashimmu.

Yace kasar Iran –ba don tana tsora , tana kiran duniya zuwa zaman lafiya a yankin yammacin Asia, kasashen yankin ne kawai suke da damar tabbatar da tsaron yankinsu ba wasu daga waje ba, ko duk a zauna lafiya ko kuma duk a zauna cikin rashin aminci.

Dangane da makamashin nukliya kuma shugaban, ya ce, Iran bata neman mallakar makaman Nukliya, kuma ba zata kyale hakkin da na mallakar makamshin nukliya ta zaman lafiya ba, ba wanda ya isa ya takaita Iran daga mallakan makamashin nukliya ta zaman lafiya ba.

Yace, wadannan kasashe wadanda suka nuna karfi da zalunci a duniya sun bar HKI tana jefa bom a kan duk wata kasa da ta bukata a yankin yammacin Asia, ta kashe fiye da falasdinawa 80k a cikin yan shekaru da suka gaba, sannan ta mallaki makaman Nukliya amma babu wani Jami’I mai bincike da ya taba zuwa can. Makaman Nukliya suka HKI masu bincike suna Iran. Wannan shi ne mummunan halin da ake ciki a duniya a yau.

Dangane da Falasdinawa kuma shugaban, ya bayyana cewa ba za’a taba samun zaman lafiya a yankin yammacin Asiya ba matukar ba’a kafa kasar Palasdinu mai zaman kanta ba. Ko an murkushe Falasdinawa a wani bangare sai sun take bullowa ta wani bangare.

Ba za’a taba samun zaman lafiya a gabas ta tsakiya ba matukar babu adalci, matukan ana daukar wasu mutane sun fi wasu daraja.

Dangane da ta’asan da sojojin HKI da Amurka suka aikata a yankin da suka dorawa kasar a ranar 28 ga watan fabraiyun da ya gabata. Shugaba Pezeshkiyan ya daga hotuna Jagoran juyin juya halin musulunci wanda suka fara kashewa a wannan yakin, da kuma Jikansa jariya wacce bata fi watanni 14 a duniya ba. Yace Amurka da HKI ne yan ta’adda na gaskiya, amma suna kiran Iraniyawa a matsayin yan ta’adda.

Yace tun ranar mutanen kasar Iran suna kan titunan kasar a dukkan darare kimani 200 da suka gabata, inda suke nuna goyon baya ga gwamnatin kasar ga sojojin kasar wadanda suke maida martani suke kuma samun nasarar a kan yan mamaya, yan ta’adda na gaskiya.

Masu sauraron karshen sharhin Kenan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted