Sanatan Amurka ya bayyana cewa: Barazanar shugaba Donald Trump ga Iran laifi ne na yaki
Wani Sanata a Amurka ya mayar da martani ga kalaman Trump masu ban tsoro game da Iran.
Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ruwaito cewa: Sanata Bernie Sanders na Amurka ya tabbatar a wani rubutu a wani dandalin sada zumunta cewa: Halaka al’ummar Iran, kamar yadda Trump ya yi barazanar yi, laifi ne na yaki da kuma aikata barna da bai kamata Amurka ta yi ba kwata-kwata.
Ya kara da cewa: “A’a, Shugaban kasa, bai kamata Amurka ta rusa al’ummar Iran ba. Wannan laifi ne na yaki da kuma aikata barna.”
Sanders ya fayyace cewa: Cin zarafin da Amurka ke yi wa Iran sun saba doka, kuma dole ne Majalisar Dokoki ta Amurka ta dauki mataki nan take don kawo karshen wannan yakin da kuma daukar matakan da suka dace.
Trump ya yi ikirarin a cikin jawabinsa mai ban tsoro a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Dole ne a yanke babban shawara game da Iran: ko dai a sanya hannu kan yarjejeniya mai kyau da wannan kasar ko kuma a rusa ta!