kungiyar NLC Ta Goyi Bayan Bukatar Ma’aikatan Najeriya

kingiyar kwadago ta najeriya ta nuna goyon bayan bukatar rage farashin man fetur da karin albashi

Wata Kungiya da ta Kunshi ma’aikatan da ke karkashin hukumomin gwamnati, ta rubuta wa shugaba Bola Ahmed Tinubu wasikar neman daukar matakan rage kaifin tsadar rayuwa da ake fama da ita a sassan kasar, wanda ke da nasaba da sake tashin farashin man fetur wanda ya tsawwala farashin kayayyaki tare da jefa rayuwar dimbin ma’aikata a cikin mawuyancin hali..

 Daga cikin shawarwarin da suka gabatar har da neman karya farashin litar mai zuwa N500, da karin albashi da kudaden alawus alawus.

Tuni babbar kungiyar kwadago ta Najeriyar NLC ta nuna cikakken goyon baya ga wannan mataki, inda sakataren tsare-tsare na kungiyar ta kasa Kwamred Nasir Kabir ya ce basa goyon bayan karin farashin man da aka samu a kasar, lura da illarsa ga walwalar ma’aikata.

Tuni dai kungiyar ta kuma bai wa gwamnatin Najeriya wa’adin nan da zuwa ranar Larabar makon gobe da ta dauki mataki kan wadannan bukatu da ta gabatar, domin a cewarta tsanantar matsin rayuwar da ake fama da shi a tsakanin ma’aikata da kuma ƴan Najeriya, na haifar da barazana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted