Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: An gudanar da tattauawa tsakanin Iran Amurka ta hanyar mai shiga tsakanin kasar Qatar
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Tawagar Iran da ke birnin New York ta bayyana a sarari sharuɗɗa da matsayin kasarta ta hanyar mai shiga tsakani na kasar Qatar.
Da yake mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na nuna kin jinin Iran a lokacin da yake jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, Baqa’i ya ce: Waɗannan zarge-zarge ne da tuhumce-tuhumce da ake maimaitawa, kuma irin waɗannan maganganun ba su samo asali daga madogara mai ƙarfi ba amma rudu ne masu rauni. Ya ƙara da cewa: Zarge-zarge ne haramtattu kuma sun yi hannun riga da dokokin ƙasa da ƙasa da ƙa’idodin diflomasiyya.
Ya bayyana cewa: Barazanar da ake yi wa ƙasar Iran da kai mata harin soja, ra’ayi ne na gwamnatin Amurka da ke nuna gamsuwa da aikata laifukan ƙasa da ƙasa. Ya ƙara da cewa: Tawagar Iran ta halarci taron sannan ta tafi, kuma, kamar yadda aka saba, wani jami’in diflomasiyya daga tawagar Iran zuwa Majalisar Dinkin Duniya yana wurin taron.
Dangane da labaran da suka shafi tattaunawar da aka yi tsakanin Iran da Amurka a New York, ya ce: Wannan hulɗar ta zo ne da nufin sanar da sharuɗɗan Iran, ciki har da kawo ƙarshen yaƙi a dukkan fannoni, dakatar da ayyukan ta’addanci na Amurka, kawo karshen killace jiragen Ruwan Iran, watsi da yaƙin tattalin arziki, sakin kuɗaɗen Iran, da sauran abubuwa.