Ci Gaban Jawabin Shugaban Kasar Iran A Majalisar Dinkin Duniya

A wani bangaren Jawabinsa a zaman babban taron Majalisar Dinkin Duniya Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A fili yake waɗanda suke kiran Iraniyawa ‘yan

A wani bangaren Jawabinsa a zaman babban taron Majalisar Dinkin Duniya Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A fili yake waɗanda suke kiran Iraniyawa ‘yan ta’adda ya tabbata cewa: Sune ‘yan ta’adda kuma suke horar da ‘yan ta’addan duniya

Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezzekian ya bayyana cewa: “Waɗanda ke kiran Iran ‘yan ta’adda, su kansu ‘yan ta’adda ne kuma suna horar da ‘yan ta’adda. Duniya ta sanin cewa: Iraniyawa ba ‘yan ta’adda ba ne, kuma suna kare kansu ne daga hare-haren wuce gona da iri. Mutanen Iran an tilasta musu kare kansu ne don haka suna yaki ne domin tsaron kare kansu a yakin da aka dora musu, kuma Iraniyawa sun yi nasarar kare kansu daga muggan sabbin makamai na fasahar Amurka da na Isra’ila da suka kai kan Iran, kuma mutanen Iran sun tsaya kyam. Ba su mika kai ga Mahara msu wuce gona da iri ba.

Amurka da Isra’ila sun kasance suna da kayan aiki don kai hari kan makarantu, asibitoci, gadoji da kayayyakin more rayuwa na Iran.

Shugaba Pezeshkian  ya tunatar da cewa: An shirye masu kayan aiki da suka hada da muggan makamai suke su kaddamar da hari kan makarantu, asibitoci, gadoji da kayayyakin more rayuwa na Iran, kuma sun yi hakan, duk da cewa hakan ya saba wa dokokin duniya. Yana mai jaddada cewa: A lokacin da ya hau mulki, a rana ta farko, makiya zaman lafiya sun kashe Ismail Haniyeh a birnin Tehran. Isra’ila tana jefa bama-bamai don kashe duk wani jami’in gwamnati da yankin da take so. A Gaza, sun kashe mutane sama da 80,000 marasa laifi kuma sun kori sama da mutane dubu ɗari, kuma suna aikata kisan kare dangi da muggan makamai da suka mallaka, amma suna kiran wasu ‘yan ta’adda da masu tayar da hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted