Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi gargadin illar daukan duk wani sabon matakin soja a yankin
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran kan Shari’a da Harkokin Ƙasashen Waje, Kazem Gharibabadi, ya bayyana cewa: Tasirin yaƙi da Iran ba zai takaita ga ɓangarorin biyu masu faɗa ba, amma zai shafi wasu ƙasashe da ƙungiyoyi. Ya jaddada cewa: Duk da cewa maƙiyan Iran za su iya fara yaƙi da ita, “amma ba za su iya kawo ƙarshenta ba.”
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya ƙara da cewa: “Maƙiyan Iran sun sha kashi a hare-haren da suka kai a baya, don haka yanzu suna neman share fagen wani harin soja ta hanyar tayar da rikici da kuma kunna wutar tashe-tashen hankula a zanga-zangar lumana.”
A babban taron da aka yi a Geneva kan kwance damarar makamai, Gharibabadi ya tabbatar da cewa: “Iran ba za ta fara wani yaƙi ba, amma za ta tsaya tsayin daka kan fuskantar duk wani makirci da ke kai hari ga tsaronta da kwanciyar hankalinta.”
Gharibabadi ya yi watsi da duk wani ikirari game da manufofin soja na shirin makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta da makaman nukiliya, ba ta neman mallakar su, kuma ba ta da niyyar yin hakan. Shirin makamashin nukiliyar Iran gaba daya yana cikin tsarin zaman lafiya ne kuma yana karkashin jagorancin wajibcin doka na kasar da kuma ka’idojin akida da dabi’u wadanda ke kin amincewa da makaman kare dangi.”