IRGC: Makaman Iran Suna Iya Zuwa Nesa Da Yankin

Mataimakin babban kwamandan dakarun IRGC ya bayyana cewa Iran zata fadada yankunan da zata kaiwa hare hare idan makiya sun kuskura sun farwa kasar da

Mataimakin babban kwamandan dakarun IRGC ya bayyana cewa Iran zata fadada yankunan da zata kaiwa hare hare idan makiya sun kuskura sun farwa kasar da yaki.

Tashar  talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Izadi yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijan ta Al-alam a nan Tehran . Ya kuma kara da cewa. Hare hare kan cibiyoyin nukliya, ko wurare masu muhimmanci a kasar, zai sa sojojin kasar su maida martani, kan makiya ba tare da bata lokaci ba. Banda haka Janar Izadi ya ce, idan makiya sun sake takalar wani yaki da kasar A wannan karon yakin zai hada da wasu yankuna wajen yammacin Asia. Banda haka martani zai kasance mai zafin gaske.

Janar  Izadi ya ce, a yau makaman jumhuriyar Musulunci ta Iran zasu iya iya wuraren nesa da kasashen yammacin Asia, kuma idan sun takali wani yaki jiragen yakinsu a wasu yankuna ba zasu tsira daga makamammu ba.

Yace a yankin ramadan mun takaita hare haremmu kan HKI da kuma kasashe 8 na yankin yammacin Asia ne, saboda sansanonin Amurka suna cikin wadannan kasashe. Amma a halin yanzu muna iya fadada yakin zuwa wajen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted