Rahotanni da muka samu daga kasar siriya sun bayyana cewa manyan kwamandojin kungiyar Ta’adda ta Daesh ta sake bayyana a garin raqqa dake arewa maso yammacin kasar siriya adaidai lokacin da rashin tsaro yake karuwa a kasar, karkashin jagorancin kungiyar hayat tahrir shams.
kasar siriya ta samu sauyi sosai karkashin tsohon mataimakin kungiyar Daesh Muhammad Jolani a fagen siyasa da na soji, yayin da sauran kungiyoyin dake hamayya da haitut tahariri shams ke ci gaba da arangama akokarin da take yi na samu iko a fadin kasar.
A yan makwannin nan wani adadi mai yawa na yan kungiyar Daesh da iyalansu sun tsare daga wuraren da ake tsare da mutanen da ake kira da yan tawayen siriya, kuma sun gudu ne bayan arangama tsakanin dakarun yan tawaye da rundunonin da ake dangantasu da maa’ikatar tsaro ta gwamnatin kasar.