Shugaban kasar Senegal Bassirou Diamaye Faye ta isa birnin Bamako domin ganawa da takwaransa na kasar akan alakar kasashen biyu.
An sa ran cewa bangarorin biyu za su tattauna batutuwa masu alaka da tsaro da kuma aiki tare da fagen soja sai kuma jigilar kayayyakin kasuwanci a tsakaninsu.
Kasar Mali dai tana shigar da mafi yawancin kaya daga kasashen waje ta hanyar tashar jiragen ruwan Dakar na kasar Senegal,sai dai an sami tsaiko saboda hare-haren masu jabun jihadi.
A farkon wannan shekarar ne dai kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso su ka sanar da cewa sojojinsu za su fara aiki tare domin kai hare-haren hadi gwiwa akan masu dauke da makamai.