Tsohon shugaban kasar Senegal Macky Sall zai koma kasarsa domin haduwa da shugaba mai ci Bassirou Diomaye Faye a karon farko, saboda ya sami goyon baya a kokarinsa na ganin an zabe shi a matsayin babban magatakardar MDD.
Ziyarar ta tsohon shugaban kasar za ta zama irinta ta farko tun a shekarar 2024 bayan rikicin da yake tsakanin bangarorin biyu. Abinda kuwa zai kai shi shi ne neman goyon baya daga gwamnatin kasarsa domin zama babban magatakardar MDD.
Shi dai Macky Sall ya wallafa wannan sakon ne a shafinsa n asada zumunta, tare da cewa zai yi tattaunawa da tuntubar wadanda ya kamata a kokarinsa na son zama babban magatakardar MDD.
Abinda kuwa zai kai shi birnin Dakar shi ne haduwa da shugaba Bassirou Faye.
A lokacin shugabancinsa an sami sabani a tsakanin shugaban kasar ta Senegal Macky Sall da kuma wanda ya gaje shi da akan karagar Mulki da kuma jam’iyyarsa.
Tuni dai aka fara gogoriyon tsayawa takarar sakataren MDD saboda nan da 31 ga watan Disamba ne Antonio Guterres zai sauka saboda karewar wa’adinsa.
A farkon watan janairu na 2027 ne ake sa ran cewa sabon wanda za a zaba a matsayin babban sakataren MDD zai fara aiki.