Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tatsuniyar wucewa ta Hormuz ba tare da wani sharaɗi ba ta ƙare tun bayan harin wuce gona da iri kan Iran
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya soki “munafuncin” da Tarayyar Turai ke yi game da dokokin kasa da kasa, yana mai tabbatar da cewa: Iran tana da ‘yancin daukar matakan kare mashigar ruwan Hormuz daga duk wani hari.
Baqa’i ya mayar da martani mai kaushi ga kalaman da shugabar kula siyasar harkokin waje na Tarayyar Turai Kaja Kallas ta yi game da ‘yancin zirga-zirga a mashigar ruwan Hormuz, yana mai bayyana maganarta game da “dokokin kasa da kasa” a matsayin “kololuwar munafunci.”
A ɓangaren shari’a da kuma al’ada, Baqa’i ya jaddada cewa: Babu wata doka a cikin dokokin ƙasa da ƙasa da ta hana Iran, a matsayinta na ƙasa mai gabar teku, ɗaukar matakan da suka dace don hana amfani da mashigar ruwa ta Hormuz don kai mata harin soja.